Friday, March 20, 2015

RANAR JUMMA'A

RANAR JUMA'A 29 Jumada-Al-Awwal, 1436 | 20 March, 2015 Dukkan yabo da godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, shi ne mafi sanin abin da kowanne dan Adam ke boyewa a zuciyarsa da abinda yake bayyanawa ina gode masa ina jinjina masa. Dukkan salati ya tabbata ga manzon Allah S.A.W shugaban dukkan halitttu gaba daya, wanda shine mai ceton kowa da kowa. Ranar juma'a itace mafi alherin dukkan wata rana da rana ta fito a cikinta. cikinta Allah ya halicci Adam, cikinta ne qiyama zata tsayu, kuma ita ranar idi ice ga musulmai. Don haka nema aka sharanta wasu abubuwa acikinta, daga ciki akwai: hudubar jumaa, wanka, fesa tirare, fita cikinta da mafi kyawun kaya da yanayi me kyau, yin kabarbari lokacin fita sallar, kusantar liman, da kuma tara tunani gaba daya domin sauraren wa’azi da ambato (wato huduba), da kuma yawaita salati ga Annabi S.A.W kamar yadda yazo a cikin wani Hadisi: ﻋﻦ ﺃﻭﺱ ﺑﻦ ﺃﻭﺱ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ: ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ: ﺇﻥ ﻣﻦ ﺃﻓﻀﻞ ﺃﻳﺎﻣﻜﻢ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ، ﻓﺄﻛﺜﺮﻭﺍ ﻋﻠﻲ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻓﻴﻪ،ﻓﺈﻥ ﺻﻼﺗﻜﻢ ﻣﻌﺮﻭﺿﺔ ﻋﻠﻲ، ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮﺩﺍﻭﺩ An karbo hadisi daga Aus Bin Aus R.A yace: Manzon Allah S.A.W yace: "Hakika daga cikin mafifitan ranakunku itace ranar jumu'a, ku yawaita salati agareni a cikinta, domin salatinku abin gittawane a gareni." Abu Dawuda ya rawaito shi. A wani hadisin kuma daga Abu Huraira (R.A) yace: Manzon Allah S.A.W ya ambaci ranar jumma'a sai yace "A Cikinta akwai wani lokaci da mutum musulmi bazai dace dashi ba alhalin yana tsaye yana sallah yana rokon Allah mabuwayi mai girma wani abu face an bashi wannan abun" kuma yayi nuni da hannunsa yana kankantar da lokacin. Bukhari da Muslim. Ya Allah ka kara mana so da kaunar Abul Qasim S.A.W tare da ikon tabbatuwa akan sunnarsa, da bin umarninsa da haninsa ameen.

Wednesday, March 11, 2015

AL’AWRA GA MACE Daga Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi

AL’AWRA GA MACE Watau duk abunda zai ja hankalin namiji zuwa ga son mace ko sha’awarta to wannan haramun ne ga mace da ta bayyana shi zuwa ga namiji ko mace mai sha’awar mata. Ita fuska da tafin hannu ba alawra bane a wurin sallah amma wurin mutane sai da sharadin basu fitinar mai kallonsu, amma a wannan zamani na fitina, mace ta fi kowa sanin abunda ya kansa maza su kalleta da sha’awa, saboda haka ya zama wajibi ta suturtashu kuma babu banbanci tsakanin mai aure da marassa aure. Wannan kuwa kamar yadda manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agaresa – yace: “Kowane dan Adam yana da nashi rabo na zina. Zinar idanu biyu itace kallo, zinar halshe Magana, kuma kunaye biyu zinarsu saurare, hannaye biyu suma suna zina, zinarsu kuwa itace kamawa, kuma kafafu biyu suna zina, kuma zinar su itace tafiya, kuma baki yana zina, kuma zinarsa itace sumbunta” Allah Ya taimake mu da matan musulmi wurin bin abinda shine alheri garemu duniya da lahira. Amin.