Sunday, March 22, 2015

INA YA KAMATA NA KALLA A JIKIN BUDURWATA ?

TAMBAYA: Malam ko ya halatta in kalli gashin macen da nike so in aura? Ko kuma don Allah malam ka taimaka kaman bayanin abunda ya halatta in kalla a jikin macen da zan aura kafin muyi aure. Na gode. Allah ya gafarta maka. AMSA: To dan'uwa ya halatta ka kalli macen da kake so ka aura, kamar yadda ya zo a cikin hadisi, inda Annabi s.a.w. yake cewa : "Idan dayanku yana neman aure, to in ya sami damar kallon abin da zai kira shi zuwa aurenta, to ya aikata hakan" Abu dawud a hadisi mai lamba ta : 2082. Malamai sun yi sabani akan wurin da ya kamata mutum ya kalla a jikin mace lokacin da ya je neman aure : 1. Akwai wadanda suka ce zai kalli fuska da tafin hannu ne kawai, saboda tafin hannu yana nuna ni'imar jikin mace, kamar yadda fuska take nuna kyau, don haka sai a takaita akan su, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai. 2. Zai kalli duk abin yake bayyana a jikin mace, don haka bayan fuska da hannu zai iya kallon duga-dugai da wuya. 3. Wasu malaman sun tafi akan cewa : zai kalleta a kayan da take sawa a cikin gida, ta fuskace shi ya kalle ta, sannan ta juya baya ya kalleta. Wannan ra'ayin shi ne ya fi dacewa, saboda ta haka mutum zai san yanayin matar da zai aura, yadda ya kamata . Saidai ba'a son yawaita kallon saboda duk abin da aka halatta saboda bukata, to ya wajaba a tsaya a gwargwadonta, wannan yasa yawaita zuwa zance da yawaita yin waya, zai iya zama haramun saboda yana iya tayar da sha'awa, sha'awa tana iya kaiwa zuwa barna Allah ne mafi sani Don neman Karin bayani, duba : Al'insaf 8\15 da Muhallah 9\161. Jamilu Zarewa 21\3\2015

Friday, March 20, 2015

MATSAYIN BIRNIN MAKA DA DARAJARSA

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM. Matsayin Birnin Makka da Darajarsa Kamar yadda Allah ya zavi wasu mutane ya ba su fifiko a kan wasu, haka su ma garuruwa da birane Allah ya fifita wasu a kan wasu. Idan kuwa ana maganar qasashe da manyan biranensu to, Makka ita ce "Ummul Qura" uwar birane da nassin Alqur'ani. Gari ne da Allah ya sanya aminci da kwanciyar hankali a cikinsa. Alqibla ce ta musulmi a duk inda suke a duniya. Zukatan muminai a ko ina suna karkata zuwa ziyarar sa. Kuma idan sun koma gidajensu nan take sai su buqaci komawa.
A nan ne xakin Allah na farko da aka gina don ibada yake. A jikinsa akwai Hajarul Aswad daga cikin duwatsun aljanna. Shi ne kaxaitaccen wuri da aka amince ma musulmi ya shafa da sunan ibada. Sallah a wannan gari tana da qarin matsayi sama da ninki 100,000 a kan wani gari duk da ba shi ba. Sai dai masallacin Manzon Allah. Shi ma Makka ta fi shi da sama da ninki xari a ladar sallah. Ma'ana Haqiqa gida na farko da aka gina domin mutane (su yi bautar Allah a cikin sa) shi ne wannan da yake a Bakka (Makka), mai albarka ne kuma shiriya ga mutane. A cikin sa akwai ayoyi bayyanannu ga talikai; matsayin Ibrahim. Wanda duk ya shiga a cikin sa ya zama amintacce.
Ba a zubar da jini a birnin Makka. Ba a farauta ko tada hankalin tsuntsu balle bil-Adama. Ba a cire ganye daga bishiya. Ba a xaukar tsintuwa sai idan za a cigita.
Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi daga xan Abbas Radhiyallahu Anhu daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam cewa, Allah ya haramta Makka, bai tava halalta ma kowa yin yaqi a cikin ta ba gabani na, haka ma ba zai halalta ma kowa ita ba a baya na. Ni ma awa xaya ce daga cikin wuni aka halalta ma ni. Don haka, ba a tsinke ganyenta, ba a yanke bishiyarta, ba a korar dabbar farauta a cikinta, ba a xaukar tsintuwarta sai ga wanda zai yi cigiya". Sai Abbas Radhiyallahu Anhu ya ce "A cire ma na Idhkhir; bishiyar da muke yin rini da ita, kuma muke amfani da ita wajen rufe matattunmu". Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya ce, ※To, ban da ita.
Albarkacin addu'ar Annabi Ibrahim Alaihis Salam a kullum ana samun ko wane nau'in abinci da kayan marmari a birnin Makka. A qarshen zamani kuwa idan Dujjal ya bayyana, Allah zai tsare wannan birnin daga qazantar takon qafafunsa kamar yadda ya tsare shi daga sharrin rundunar Giwaye.
Bukhari da Muslim sun karvo hadisi daga Anas xan Malik Radhiyallahu Anhu daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam cewa, "Babu wani gari da Dujjal ba zai shiga ba sai Makka da Madina. A lokacin bayyanar sa babu wata kafa a cikinsu (Makka da Madina) sai Mala'iku sun yi sahu a kai suna kare ta. Sannan Madina zata yi girgiza uku da mutanen da ke cikin ta. Duk wani munafiki ko kafiri sai ya fita".
A wannan tsarkakakken gari ne aka haifi shugabanmu kuma shugaban ma'aika Muhammadu xan Amina, Sallallahu Alaihi wa Sallam.

RANAR JUMMA'A

RANAR JUMA'A 29 Jumada-Al-Awwal, 1436 | 20 March, 2015 Dukkan yabo da godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, shi ne mafi sanin abin da kowanne dan Adam ke boyewa a zuciyarsa da abinda yake bayyanawa ina gode masa ina jinjina masa. Dukkan salati ya tabbata ga manzon Allah S.A.W shugaban dukkan halitttu gaba daya, wanda shine mai ceton kowa da kowa. Ranar juma'a itace mafi alherin dukkan wata rana da rana ta fito a cikinta. cikinta Allah ya halicci Adam, cikinta ne qiyama zata tsayu, kuma ita ranar idi ice ga musulmai. Don haka nema aka sharanta wasu abubuwa acikinta, daga ciki akwai: hudubar jumaa, wanka, fesa tirare, fita cikinta da mafi kyawun kaya da yanayi me kyau, yin kabarbari lokacin fita sallar, kusantar liman, da kuma tara tunani gaba daya domin sauraren wa’azi da ambato (wato huduba), da kuma yawaita salati ga Annabi S.A.W kamar yadda yazo a cikin wani Hadisi: ﻋﻦ ﺃﻭﺱ ﺑﻦ ﺃﻭﺱ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ: ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ: ﺇﻥ ﻣﻦ ﺃﻓﻀﻞ ﺃﻳﺎﻣﻜﻢ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ، ﻓﺄﻛﺜﺮﻭﺍ ﻋﻠﻲ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻓﻴﻪ،ﻓﺈﻥ ﺻﻼﺗﻜﻢ ﻣﻌﺮﻭﺿﺔ ﻋﻠﻲ، ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮﺩﺍﻭﺩ An karbo hadisi daga Aus Bin Aus R.A yace: Manzon Allah S.A.W yace: "Hakika daga cikin mafifitan ranakunku itace ranar jumu'a, ku yawaita salati agareni a cikinta, domin salatinku abin gittawane a gareni." Abu Dawuda ya rawaito shi. A wani hadisin kuma daga Abu Huraira (R.A) yace: Manzon Allah S.A.W ya ambaci ranar jumma'a sai yace "A Cikinta akwai wani lokaci da mutum musulmi bazai dace dashi ba alhalin yana tsaye yana sallah yana rokon Allah mabuwayi mai girma wani abu face an bashi wannan abun" kuma yayi nuni da hannunsa yana kankantar da lokacin. Bukhari da Muslim. Ya Allah ka kara mana so da kaunar Abul Qasim S.A.W tare da ikon tabbatuwa akan sunnarsa, da bin umarninsa da haninsa ameen.

Wednesday, March 11, 2015

AL’AWRA GA MACE Daga Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi

AL’AWRA GA MACE Watau duk abunda zai ja hankalin namiji zuwa ga son mace ko sha’awarta to wannan haramun ne ga mace da ta bayyana shi zuwa ga namiji ko mace mai sha’awar mata. Ita fuska da tafin hannu ba alawra bane a wurin sallah amma wurin mutane sai da sharadin basu fitinar mai kallonsu, amma a wannan zamani na fitina, mace ta fi kowa sanin abunda ya kansa maza su kalleta da sha’awa, saboda haka ya zama wajibi ta suturtashu kuma babu banbanci tsakanin mai aure da marassa aure. Wannan kuwa kamar yadda manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agaresa – yace: “Kowane dan Adam yana da nashi rabo na zina. Zinar idanu biyu itace kallo, zinar halshe Magana, kuma kunaye biyu zinarsu saurare, hannaye biyu suma suna zina, zinarsu kuwa itace kamawa, kuma kafafu biyu suna zina, kuma zinar su itace tafiya, kuma baki yana zina, kuma zinarsa itace sumbunta” Allah Ya taimake mu da matan musulmi wurin bin abinda shine alheri garemu duniya da lahira. Amin.

ALHAJRUL-ASWAD (DUTSE MAI ALBARKA)

Hadisi ya tabbata cewa wannan dutse daga cikin Aljannah yake, kuma lokacin da aka saukar dashi fari ne, kal, yawan sabon mutane yasa ya zama, baki, wannan dutse, yasha gwagwarmaya iri-iri, a tsawon tarihi, lokacin da kuraishawa zasu sabinta ginin kaabah, lokacin Manzon Allah saw, yana da shekara talatin da bakwai, sunyi sabani, gamai da wanda zai dora wannan dutse. karshe, suka amince sa cewa, duk wanda ya fara shigowa, shine zaiyi hukunci, kuma zasu yarda da hukuncinsa, sai Manzon Allah saw ya fara shigowa, kuma dukkansu, sukayi farin ciki, da zuwansa, saboda sun sanshi, da gaskiya, da Amana, da Adalci, sai ya nemi, su nada wakilai daga ko wacce kabila, ya shinfida, mayafinsa, ya dora dutsan akai, yace ko wane wakili ya kama gefe, daya, su daga tare, sukai wajan, shi kuma ya daidaita shi, , Manzon Allah saw yace, wannan dutsan zaizo ranar a kiyama da ido da harshe zaiyi sheda ga duk ya sunbace shi, wannan dutse yana da sunnoni guda biyar 1- Ashafe shi da hannu, ya sunbace shi, yayi kabbara 2-Idan ba hali sai ya tabashi, ya sunbaci hannunsa 3- Idan ba hali, sai ya tabashi da sandarsa sai ya sunbaci inda ya taba da sandar. 4- Idan haka bata samu ba, sai ya nuna shi da hannu, yayi kabbara, ba tare da ya saunbaci hannunba. 5- Idan babu cunkoso, yana iya yin sujjada akansa.

Tuesday, March 10, 2015

SHEDAR ZUR ZUNUBI CE MAI GIRMA.

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI. Allah maxaukakin Sarki Ya ce: Ma'ana: Saboda haka ku nisanci qazantar gumaka, kuma ku nisanci shedar Zur. Kuna masu tsayuwa ga gaskiya domin Allah, ba masu yin shirka da Shi ba” (22:30-31). Haka kuma Abdurrahaman xan Abubakar Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, mahaifinsa ya ce: Wata rana muna zaune tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai ya ce : Kuna so in ba ku labarin manya- manyan zunubbai? Ya ko maimaita tambayar har sau uku. Sa'annan ya amsa masu da cewa: 1) haxa Allah da wani a cikin bauta, 2) qin uwaye… Manzon Allah yana gincire sai ya tashi zaune. Sannan ya ce: 3) Da kuma Shedar Zur. Mai riwayar (Sayyidina Abubakar) ya ce, Annabi ya yi ta maimaita na ukun nan har muka yi sauraren ya dasa aya.” (Bukhari: 5/261) Gargaxi da jan kunnen mutane a kan su nisanci Shedar Zur abu ne da shari'a ta faxa ta maimaita ta kuma nanata, saboda irin yadda mutane ba su xauki yin hakan bakin komai ba. Duk da yake kuma an fahimci cewa qiyayya da gaba ne kan sa wasu mutane faxa wa wannan haramiya don fashe haushinsu akan wani wanda suke adawa da shi. Amma kuma hakan ba ya zama hujja gare su. Musamman idan aka yi la'akari da irin mummunan sakamakon da tagarar ke haifarwa wanda ya haxa da; i) Sa mutane da yawa hasarar wasu haqqoqa nasu, ii) jefa wasu mutane da yawa cikin baqar musiba ba su ji ba su gani ba, iii) share wa wasu mutane da yawa hanyar samu da mallakar abin da ba su cancanta ba. Da sauransu. Wani babban misalin da ke tabbatar da irin yadda mutane ba su xauki Shedar Zur bakin komai ba shi ne abin da kan faru a wasu kotunanmu a yau. Nan take wani zai ce wa wani “Zo ka shede ni, ni kuma in shede ka”. Alhali kuwa a wannan lokacin ne suka fara haxuwa. Ka ga kenan ko wanensu zai shedi xaya a kan abin da bai san komai game da shi ba, balle ya iya bayanin yadda ya faru dalla dalla. Wato kamar ya shede shi a kan mallakar wani fili ko gida, ko ya wanke shi daga wani bashi, alhali bai ko tava ganinshi ba kafin yau a kotu. Turqashi! Wannan ita ce tantagaryar qarya da Shedar Zur. Domin kuwa Allah Subhanahu Wa Ta'ala cewa ya yi a yi sheda a kan abin da aka sani: Ma'ana: Kuma bamu yi sheda ba face da abin da muka sani. Kuma bamu kasance masu kiyaye aibi ba. (12:38)

ROQO BA BUKATA DA CIN DUKIYAR HARAMUN MANYAN ZUNUBAI

CIN DUKIYAR HARAM BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM. Da yawa mutanen da tsoron Allah ya yi wa kaxan a zukata, ba su damu da ta ko wace hanya za su sami kuxi ba, balle wadda za su kasha su a cikin ta. Abin da kawai ya dame su, shi ne yadda ajiyarsu ta banki za ta qara kauri, koda ta hanyar haramiya ce. Saboda cika wannan guri, sai su shiga wawure kuxaxen bayin Allah da suke amana a hannun su. Wasu kuma su kama `yan sace-sace ko fashi da makami ko damfara ko haramtattar sana'a kamar Riba, ko cin kuxin marayu, ko bokanci. Waxansu kuma sukan kama `yan tabanjamanci ko waqa, ko tatsar taskar musulmi, ko tava kayan mutane, ko yaudararsu ta hanyar karvar kayan da qarfi, ko tsawwala wa kayan da suke sayarwa farashi. A yayin da wasu kuma ke tsira sana'ar barace- barace ba da wani dalili ba. Ga su nan dai. Da kuxin da waxannan mutane suka samu ta waxannan hanyoyi za su sayi abinci ko tufafi da ababen hawa, ko su gina gidaje, ko su kama haya, wasu ma har su sayi kayan alatu su zuba a gidajen. Alhali kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Duk tsokar jikin da ta ginu da haramun wuta ce mafi cancanta da ita” (Xabarani: 19/136). Kafin haka kuma a Ranar qiyama, Allah zai tambayi ko wane mutum a kan yadda ya sami dukiyarsa da yadda ya kashe ta. Ta haka sai kowa ya haxu da sakamakonsa daidai da aikinsa. Da wannan muke kiran duk wanda ya san cewa akwai wata dukiya hannunsa ta haram ya yi gaggawar rabuwa da ita, ya mayar wa mai ita idan ya san shi, ya kuma nemi gafarar Allah. Kafin Ranar da kuxi ba su da wani amfani sai dai aikin qwarai. Nau'in zunubi na gaba shine ROQO BA BUKATA Sahlu xan Hanzalata Radiyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya roqi mutane kuxi alhali yana da abin da ke isar sa buqata, to yana roqar ma kansa garwashin wuta ne kawai”. Sai sahabbai suka tambayi Manzon; “Mene ne miqidarin abin da za a ce ya ishi mutum buqata har ya hana shi roqon qari? Sai ya karva masu da cewa: “Idan ya mallaki abin da zai ci abincin rana da na dare” (Abu dawuda: 2/281). Haka kuma xan mas'udu Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ke roqon mutane kuxi alhali yana da abinda ke isar sa biyan buqata, zai tashi Ranar qiyama fuskarsa da farxe- farxe” (Ahmad; 1/388). Duk da irin wannan tanadi da shari'ah ta yi wa mai roqo ba da wata buqata ba. Wasu mutane a yau, sun sami sandar roqe-roqe har ma a masallaci. Inda zasu je su dami mutanen da ke sallah da salati babu li babu la. Su kan yi haka ne kuma ta hanyar shimfixa koke- koke na qarya. Wasu daga cikin su ma har takardun qarya suke yawo da su a masallatan sana damun mutane da dogon turanci. Wasu kuma iyalansu suke rarrabawa a masallatan don gudanar da wannan mugunyar sana'a. Ba su wannan masallaci ba su wancan. Alhali kuwa wasu daga cikinsu Allah ne kawai ya san iyakar abin da suka mallaka. Sai kuwa idan sun mutu, a yi ta jin sun bar kaza sun bar kaza. Alhali a lokacin da suke waxancan roqe- roqe suna rufe damar wasu mutane ne, da ba su mallaki komai ba, amma tsoron Allah da tsaron mutunci sun hana su fitowa su roqa. Mutane kuma zaton suke yi sun wadata. Qarshe sai a xauki abin da ya kamata a ba su a ba waxannan jeqaqqin.

Friday, February 13, 2015

HUKUNCIN BIKIN RANAR MASOYA (VALENTINE’S DAY)

Bikin ranar masoya ta duniya ana yinta ne sau xaya a shekara, a ranar 14 ga wata Fabareru (14 Febuary) ta samo asali ne daga masu bin addinin kiristanci a shekaru xari biyar 500 bayan tafiyar Annabi Isah alayhi salatu wassalam aka fara shi, wanda ya qirqiro wannan tunvelen shi ne wani qaton kafiri ne mai suna Fafaroma Gelasius Sanadiyar kiranta da wannan suna shine da an hana sojojin kiristoci yin aure ne daga baya aka basu izini da suyi auran su. A wannan rana ana yanka karnuka da awaki da aladu sai a samo qartai majiya qarfi guda biyu su shafe jikin su da jinin waxannan dabbobin, bayan haka sai su wanke jikinsu da madara, waxannan qartin za a karramasu saboda shafa jinin da suka yi sai a basu ‘yan mata su zava. A wannan ranar suna sanya jajayen kaya da jan takalmi suma dabbobin jajaye suke samowa, suna sayen jajayen furanne ana aikawa da su ga masoya da takardan gaisuwa (Greeting card) xauke da huton Mala’ika da fikafikai guda biyu (wannan qarya ce domin ba bu wanda ya tava ganin mala’ika acikin su) a wannan rana zina ba laifi ba ne a wuri su. Haramun ne a musulinci yin bikin ranar masoya (Valentine’s Day) domin shi musulmi kullun yana nuna soyayya ga matar sa, kuma mu a wajen mu haramun ne yin zina Allah Ya yi tattalin azaba mai tsanani ga mai yin zina in bai tuba ba kuma harun ne mu a musulinci cin naman alade balle har mu shafa jinin alade ajikin mu, shima cin naman kare haramun ne balle a shafa jininsa. Shafa jijin dabobi ajiki ya iya bayuwa ya zuwa ga shirka, Allah ya kyauta. Sayan Greeting card shima bai halasta ba ko ba a wannan ranan ba domin koyi ne da Kafirai sune su ka qirqiro Greeting card, haka sanya jan tufafi a ko wane lokaci haramun ne, haramun ne inji Annabi sallalLahu alayhi wa alhi wasallam ya ce jan kaya na kafirai ne duba Zadul Ma’ad bai halasta ba musulmi ya sanya jan kaya. An tambayi babban Malaml Sheikh Muhammad Usaymin hukuncin bikin ranar masoya ta duniya sai ya amsa da cewa haramun ne yin wannan bikin kuma limamai su gaya wa mutane haramcinsa da bala’in da ke cikin ta. Abin baqin ciki a yau ‘yan mata da ke makarantun gaba da sakandire (University) da maza waxan da basu san addini ba zaka ga suna sayan Greeting card suna ba ‘yan mata yin haka haramun ne. Yin wannan bikin ya sava wa musulinci ya kamata a tsoratar da ‘Yan Boko su gane sharrin shi, kuma dasisa ce ta maqiya addinin Allah, Allah ya kyauta amin. kuma muna kira ga iyaye su kula da ‘ya’yansu domin kuwa koyi ne da kafirai yin wannan biki, Allah ya shirye mu. Abin baqin ciki zaka ga a makarantun gaba da sakandire (Universities) maza da mata suna wa junan su murnan zagayowar ranar masoya, ko kaga an rubuta a Allan sanarwa (Notice Board) ana ma xalibai murnanzagayowarranar masoya (Valentine’s Day) yin haka kuskure ne babba kuma sava ma koyarwan manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ne, ‘yan uwa maza da mata su ji tsoron Allah su bar wan tunvelen, na kafirai ne ba nanu ba. Sheikh Munajjid ya yi littafi masamman mai magana akan haramcin bikin ranar masoya ta duniya, jeka yanar gizan sa zaka samu littafin nasa. Allah yasa mu dace ameen.

Tuesday, February 10, 2015

IMANI DA TAURARI SHIRKA CE

IMANI DA TAURARI SHIRKA CE Zaidu xan khalidu al-juhani ya riwaito cewa:“Wata rana a Hudabiyya, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba mu sallar safe, bayan an xauke ruwan sama, da aka kwana ana yi. Da ya qare sallar ya juyo ya fuskance mu. Sai ya ce: ko kun ji abin da Unbangijinku ke faxa? Muka ce: Allah da Manzonsa kaxai ke da sani.Daga nan sai ya ce:“Allah Ya ce ne: Wayewar garin nan wani bawa nawa ya yi imani da ni, wani kuma ya kafirce mani. Duk wanda ya ce:“Ruwan nan Allah ne Ya shayar da mu a cikin ikonsa da rahamarsa”.To shi ne wanda ya yi imani da ni, ya kafirce ma taurari. Shi kuwa wanda ya kafirce mani ya kuma yi imani da taurari shi ne wanda ya ce: “Tauraruwa kaza da kaza ne suka shayar da mu wannan ruwa (Buhari: 2/333). Haka kuma duk wanda ya karanta jadawalin abubuwan da za su faru na gaibi wanda ake kirdado dabra da kaiwa da komowar taurari, a cikin wata jarida ko mujalla, ya kuma yi imani da abin to, babu shakka shi ma mushriki ne. Savanin wanda karantawa kawai ya yi don nishaxi. Shi mai laifi ne kawai. Dalili kuwa shi ne, ba abu ne yardadde a shari'a ba, mutum ya nemi samun wani nishaxi ta hanyar karanta wasu abubuwa da suka qunshi Shirka. Domin shexan na iya amfani da wannan dama ya tuqa masa tuwon tulu, a wayi gari ya faxa cikin mushrikai.

Wednesday, February 4, 2015

MENENE IMANI

Furuci ne da harshe tare da kuduri a zuci hada da aiki da gabbai, yana karuwa, yana kuma raguwa. Allah Makaukaki yana cewa: Ma'ana: ((Ba wasu ba ne muminai face wadanda da zarar an kira Allah sai zukatansu su razana, idan kuma aka karanta musu ayoyinSa sai su kara musu imani, kuma ga Allah kadai suke dogaro. Su ne wadannan da suke tsaida sallah kuma suke ciyarwa daga abin da Muka azurta su da shi. Wadannan su ne muminai na gaskiya, suna da darajoji a wajen Ubangijinsu tare da gafara da arziki mai yawa). (Anfal: 2-4). Allah Madaukaki ya ce: Ma'ana: ((Duk wanda ya kafirce wa Allah da Mala'ikunSa da LittattafanSa da Ranar Lahira, to hakika ya bata bata mai nisa)). (Nisa'i: 136) Saboda haka akwai imani da harshe; kamar zikiri, addu'a, umarni da kyakkyawan aiki, hana mummunan aiki, karatun Alkur'ani da makamantansu. Akwai kuma imani da zuci; kamar kudurce kadaitakar Allah a cikin rububiyarSa (wato: mulki da halitta) da kakaitakarSa a cancantar bauta, da kadaitakarSa a sunayenSa da siffofinSa, da kudurce wajabcin bautar Allah shi kadai ba tare da an hada shi da wani abin bauta ba, da sauran abubuwan da suke da alaka da zuciya kamar niyyoyi da manufofin ayyukan bayi. Haka nan (ayyukan da malamai ke kiransu) "ayyukan zuci" suna shiga cikin imanin da a ke yi da zuciya; Misalinsu shi ne: son Allah, tsoronSa, komawar zuciya gare Shi da dogaro da Shi, da makamantansu. Daga cikin abubuwan da sunan imani ya kunsa (bayan aikin harshe da na zuciya) akwai ayyukan gabbai; irin su sallah, azumi, da dai sauran rukunan musulunci, da jihadi saboda daukaka kalmar Allah, neman ilimi da makamantansu. Allah Madaukakin Sarki yana cewa: Ma'ana: ((Idan aka karanta musu ayoyin (Allah) sai su }ara musu imani ..)). (Anfal: 2) A wani wajen kuma Allah cewa ya yi: Ma'ana: (( (Allah) Shi ne wanda ya saukar da nutsuwa a cikin zukatan Muminai domin su kara imani tare da imanin da suke da shi)). (Fathi: 4) Imani yana daduwa a duk lokacin da bawa ya kara ayyukan da'a ga Allah ya yawaita ibada, yana kuma raguwa a duk lokacin da da'arsa da ibadarsa suka ragu, kamar yadda aikata sabo ma yake tasiri a kan imani; har ma idan sabon ya kai babbar shirka ko babban kafirci to sai ya warware asalin imani ya bata shi, idan kuma bai kai haka ba to sai ya hana imanin kai wa matakin da yake wajibi ne ya kai shi, ko kuma ya bata shi ya raunana shi. Allah Madaukaki yana cewa: Ma'ana: ((Hakika Allah baya yafe (laifin) shirka da shi, (amma) kuma yana yafe duk abin da bai kai haka ba ga wanda ya so yafewa)). (Nisa' 48). Allah Ta'ala ya kara cewa: Ma'ana: ((Suna rantsewa da Allah cewa ba su fa]i komai ba, alhali sun fa]i kalmar kafirci, kuma (saboda haka) sun kafirce bayan da sun musulunta)) (Tauba: 74) Annabi (s.a.w) kuma ya ce: Ma'ana: ((Mazinaci baya yin zina -a lokacin da yake cikin yin zinar- alhali yana tare da imani, haka nan shi ma barawo baya yin sata tare da imani -a daidai lokacin da yake yin satar, shi ma mai shan giya ba ya shanta a daidai lokacin da yake shanta alhali yana da imani)). Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

RUKUNAN IMANI

Rukunan Imani su ne: Imani da Allah da Mala'ikunSa da LittafanSa da ManzanninSa da Ranar Lahira da kaddara; alherinta da sharrinta. Allah Madaukakin Sarki ya ce: Ma'ana: ((Sai dai (mai) biyayya (ga Allah shi ne) wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira da Mala'iku da Littafai da Annabawa)). (Bakara: 177) Haka nan Allah Madaukaki ya ce: Ma'ana: ((Manzo ya yi imani da abin da aka saukar masa daga Ubangijinsa haka nan Muminai; kowa -daga cikinsu- ya yi imani da Allah da Mala'ikunSa da LittattafanSa da ManzanninSa, (suna cewa) "Mu ba ma banbanta tsakanin manzannin naSa, kuma suka ce: "mun ji mun bi, ka gafarta mana ya Ubangijinmu, kuma gare ka ne makoma take"). (Bakara: 285) Allah Madaukaki yace: Ma'ana: ((Hakika Mu, kowanne abu mun halicce shi ne da wani tsari)). (kamar: 49) Annabi (s.a.w) ya ce: Ma'ana: "Imani shi ne ka yarda da Allah da Mala'ikunSa da LittattafanSa da ManzanninSa da Ranar Lahira, kuma ka yarda da kaddara; alherinta da sharrinta".

Tuesday, February 3, 2015

***SIHIRI, BAYAR DA SA'A DA FADIN GAIBU DUKKANSU SHIRKA NE***

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinqai. Godiya da yabo masu yawa sun tabbata ga Ubangiji, Sarkin nan da Ya halicci halitta daga babu, Ya kuma halicci sammai bakwai da qassai bakwai, Ya kuma halicci mutuwa da rayuwa don a iya gane masu kyawawan ayyuka. Kuma tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta, shi ne Manzonmu Annabi Muhammad, tare da jama'ar gidansa, da sahabbansa baki xaya. Bayan haka, wannan bayani na sihiri ko kuma fadin gaibu kusan na taba wallafa shi ko dai a facebook ko kuma a xadya daga cikin shafukan yanar gizon mu. Sihiri wani na'ui ne na kafirci, kuma Shirka ne. Yana kuma daga cikin zunubai guda bakwai da ke durmuyar da mutun a cikin wuta. Kuma babu wani amfani da ake samu a cikinsa. Hasali ma ba abin da yake haifarwa ga wanda aka yi wa shi illa hasara da ci baya. Allah Subhanahu Wa Ta'alaYa gaya mana matsayin masu koyon sa. Ya ce: Ma'ana: Kuma suna neman ilimin abin da yake cutar da su, kuma ba ya amfaninsu (2:102). A wata ayar kuma Ya ce: Ma'ana: Kuma masihirci ba ya cin nasara a duk inda ya je (20:69). A wata ayar kuma Allah Subhanahu Wa Ta'alaYa tabbatar da cewa duk wanda ke sihiri da tsafi kafiri ne. Ya ce: Ma'ana: Kuma sulaimanu bai yi kafirci ba, kuma shaixanun su ne suka yi kafirci, (Saboda) suna karantar da mutane sihiri da abin da aka saukar da shi a kan mala'iku biyu a Babila; Haruta da Maruta. Kuma babu wanda suka sanar sai sun ce:“Mu fa fitina ne, saboda haka kada ka kafirta”. (2:102). Bayan wannan kuma hukuncin mai sihiri a duniya shi ne kisa, kuma duk abin da ya samu daga wannan sana'a tasa qazantatta, shi ma haram ne. Amma kuma duk da irin wannan mugun matsayi na mai sihiri, sai ka taras da wasu musulmi, saboda kantar jahilci da tsatsarsa, da raunin imani da ke tattare da su, suna ziyarar masu wannan mugunyar sana'a don neman su taimake su, su xauki fansa a kan wani ko kuma don su karya wani makaru da wani ya yi masu. Alhali kuwa kamata ya yi su fuskanci Allah Subhanahu Wa Ta'alasu nemi taimakonsa a kan waxannan al'amurra da makamantansu. Ta hanyar karanta wasu surori na Alqur'ani kamar Falaqi da Nasi. Haka su ma masu bayar da sa'a, ta hanyar bayar da labarin abin da zai faru. Su ma kafirai ne. Domin suna raya cewa sun san gaibi. Alhali kuwa babu wanda ya san gaibi sai Allah. Mafi yawan masu irin wannan sana'a sukan yi amfani ne da qarancin ilimi da wayewar wasu mutane, su karve masu kuxaxe. Sai ka ga suna `yan zane -zane ga qasa, suna jefa xiyan wuri suna karanta wasu surkulle. Wasu kuma a qasashen Turai suna wasa da kofunan Gahawa da wasu `yan kwalayen qarau da madubbai, da makamantansu. Amma kuma a mafi yawan lokuta, sau xaya ne sukan yi nasara daga cikin sihiri xari da suke yi, sauran xari ba xayan kuma, sun sha kunya a cikinsu. Duk da haka, irin waxancan jahilan mutane sai su mayar da hankali a kan sihirin nan guda da qaddara ta riga fata a cikin sa, su manta da Casa'in da tarar. Take Sai ka ga suna ta yin tururuwa a garaken masihirtan, suna neman su gaya masu ko akwai sa'a a cikin wani aure ko kasuwanci da suke shirin qullawa. Ko su taimaka masu su gane wani abu nasu da ya vata da wasu abubuwa masu kama da wannan. A qa'idar shari'ar musulunci kuwa gaskata mai sihiri kafirci ne. Kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce:“Duk wanda ya je wurin wani boka ko mai sihiri, ya kuma gaskata shi, to, ya kafirce wa abin da aka saukar ga Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama(Ahmad: 2/429). Idan kuwa har zuwa wurinsu kawai mutun ya yi, ba don ya yi imani da abin da suke yi ba, ba kuma don ya yi amanna cewa sun san gaibi ba. A'a ya dai tafi ne don tantancewa da ganarwa idonsa, ko don wani abu mai kama da wannan, to bai zama kafiri ba. Amma dai ya yi babbar hasara. Don Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallamaya ce: Duk wanda ya je wurin wani mai sihiri ya kuma tambaye shi wani abu to, ba za a karvi Sallarsa ba har kwana arba'in (Muslim: 4/1751). Amma duk da haka wajibi ne ya ci gaba da Sallar, yana kuma neman gafarar Allah a kan laifin. Allah Ubangiji ya shiryar damu tafarkin gaskiya, ya kuma tsare mana imaninmu ameen.

Sunday, January 4, 2015

DALILAI TAKWAS DA SUKA HANA YIN MAULIDI.

sayyidul-istighfar-v1.jpg
DALILAI TAKWAS DA SUKA HANA YIN MAULIDI. 1✏ Maulidi baya daga cikin Shariah, Yan Shi'a Fadimiyya ne suka kirkiro shi a Egypt.
2✏ Masana tarihi sun tafka sabani game da hakikanin rana da watan da aka haifi Annabi SAW. Wasu suka ce a Ramadan, wasu suka ce a Shabaan wasu kuma suka ce a Rabi ul awwal.
3✏ Ta yaya zamuyi farin ciki da murna a ranar 12th Rabi al Awwal bayan a ranar ne Annabi S.A.W ya bar duniya? kuma babu sabani kowa ya yarda da hakan.
4✏ Bikin murnar zagayowar ranar haihuwa bashi da asali cikin Musulunci. Musulunci ya hana wannan.
5✏ Wannan biki baya daga Sunnah ko kuma Qur'an. Dukkan Ibadar da bata daga dayan biyun nan, to ba musulunci bane... Annabi SAW, "Na hore ku da kuyi riko da sunna ta da kuma sunnar khalifofina shiryayyu, ku guji fararrun al'amura, domin dukkan fararrun al'amura Bid'ah ne kuma dukkan Bid'ah bata ce. (Tirmizi 2676)"
6✏ Allah yana cewa a cikin [Surah al Maidah 3]. "A yau na kammala muku addininku." Tunda kuwa Musulunci ya cika ya kammala, waye kuma yake da wani da zai karo wani abu a cikinsa?
7✏ Bikin maulidi koyi ne da Yahudawa da Nasara. Yahudawa na murnar haihuwar Uzair, Nasara suna murnar haihuwa Annabi Isa AS. Bayan kuma Annabi SAW yace, "Duk wanda yayi koyi da wata al'umma to yana cikinsu. (Abu Dawood)"
8✏ Annabi SAW yace, " Ku bambamta ku sabawa mushirikai. (Sahih Muslim)"
bism01.jpg
Murnar biki sabuwar shekara da wasu yan uwa daga cikin Musulmai keyi, ya sabawa shari'ah. Kai bama shekarar miladiyya ba ko shekarar hijiriyya ce yin bikin baya bisa tafarkin Sunnar Annabi S.A.W0. Babu abinda aka samu cikin karnoni ukun farko na Musulunci mafiya daraja a wajen kowanne Musulmi, na daga yin biki a ranar daya ga watan Al-Muharram, ballantana kuma ranar daya ga January.®

Tuesday, December 23, 2014

KYAUTAR BIKIN CHRISTMAS: HALAL KO HARAM♥♥♥

Da yawa musulmi suna tambayar shin ko ya halatta su karbi kyautar kiristoci a ranar kirsimeti, musamman wandanda suke zaune lafiya tare da su, ko suke aiki a guri daya. Ga bayanin da Malamai suka akai: 1. Baya halatta ga musulmi ya nuna farincikin sa da wannan ranar, ta hanyar aikawa da gaisuwa ko kyauta ko furanni, ko makamantansu. 2. Ba ya halatta gare shi ya ci abin da aka yanka da sunan wannan rana. 3. Ya halatta ya karbi kautar da za su ba shi a wannan ranar. Kamar yadda ya halatta gare shi ya ci abin da za su ba shi wadanda ba yankawa ake yi ba. Kamar kayan marmari. 4. Dalili kuwa shi ne: A) Baihaqi ya ruwato a cikin littafinsa As-Sunanul Kubra 9/234 cewa, Muhammad bn Sirin ya ce, an kawo wa Ali (ra) kautar idin majusawa Nairuz. Sai ya ce, menene wannan kuma? Sai suka ce masa, ya sarkin muminai yau ranar idin Naruz ce. Sai ya ce, to kullum ma su yi 'Fairuz'. Wato ya karba, tare da nuna ya ji dadin kyautar. B) Ibn Abi Shaibah a cikin littafinsa Al-Musannaf 5/126 daga Sahabin nan Abu Barzata Al-Aslamy cewa, yana da makota majusawa, kuma a duk ranar bukukuwansu suna aiko masa da kaututtuka gidansa, sai yakan cewa iyalinsa, abin yake kayan marmari ne to ku ci, wanda kuma ba su ba, to ku mayar musu kayansu. C) Hakanan ya ruwaito 5/126 cewa, wata mata ta tambayi Nana A'isha ta ce, muna tare da mata majusawa masu sana'ar shayar da jarirai, to duk ranar idinsu suna aiko mana da kyauta. Sai A'isha (rah) ta ce mata, abin da aka yanka domin wannan ranar kada ku ci. Ku ci kayan marmari na itatuwa. Ibn Taimiyya ya ce, wannan ya nuna idinsu ba shi da wani tasiri wajen ya hana a karbi kyautarsu. Karbar kautarsu a ranar idinsu da ranar da ba idin ba duk hukunci daya ne, domin wannan ba shi ne taimaka musu ba akan aikinsu na kafirci. Duba Littafinsa Iqtidha' Siratil Mustaqim 2/52. Ba ya halatta musulmi ya taimaka da yi musu yanka a wannan ranar. Kuma koda musulmi ne ya yanka musu ba za ci ba. Allah ka shiryar da mu tafarkinka madaidaici. - Shaykh Dr. Muhd Sani Umar Abdullahiabubakar06@gmail.com

Friday, December 5, 2014

INA ALLAH YAKE (1), at Faringida's moblog

INA ALLAH YAKE (1), at Faringida's moblog http://moblog.net /view/994750/ina-allah- yake-1

Sunday, August 10, 2014

MA'ANAR KALMAR SHAHADA (1)

Shahadu biyu sune: Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, da shaidawa lallai Annabi Muhammadu (S.A.W) Manzon Allah ne. Kuma sune tushen addinin Musulunci kuma gimshiqinsa na farko, wanda dashine bawa ke shiga Addinin Musulunci, saboda haka, duk wanda bai shaida da waxannan shahadu biyuba, to shi ba Musulmi bane Abdullahi xan Umar (Allah Ya qara musu yarda) ya ruwaito daga Annabi (S.A.W) cewa yace: "An gina musuluncine akan (gimshiqai) biyar, shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da aikin hajji, da azumtan watan ramadana." Bukhari da Muslim ne suka ruwaitoshi. Saboda haka, abu nafarko daya wajaba ga bawa ya fara sani acikin addinin Musulunci shine; gimshiqinsa na farko, wato ya san ma'anar Kalmar shahada da hukunce hukuncenta. Kuma Yayinda Annabi (S.A.W) ya aika Mu'azu xan Jabal zuwa (qasar) Yaman amatsayin mai kira (zuwa ga Allah) kuma malami yace masa: "Lallai zaka tafine zuwaga wasu jama'a daga ma'abuta littafi, saboda haka kafarada kiransu zuwaga shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma lallai ni (Muhammadu) manzon Allah ne, idan sukayi biyayya akan haka, sai ka sanardasu cewa Allah Ya farlanta salloli biyar akansu cikin kowane yini da dare…" zuwa qarshen hadisin. Imamu Muslimne ya ruwaitoshi daga hadisin Abdullahi xan Abbas Hakananma Imamul Bukhari ya ruwaito shi da lafazin; " Abu na farko da zaka kirasu zuwa gareshi ya kasance shine su kaxaita Allah. Kuma bayanin wannan ya zo acikin hadisin (da akafi sani da hadisin) Jibril mai tsayinnan wanda (Jibrilu)ya tambayi Annabi (S.A.W) gameda martabobin addinin Musulunci; Imani, Musulunci da Ihisani, sannan sai Annabi (S.A.W) yace wa sahabbansa- kamar yadda yazo aqarshen hadisin: "Wannan Jibirilune yataho gareku don ya karantar daku addininku". Saboda haka, abubuwa nafarko da suka wajaba asani cikin al'amuran addini, sune abubuwanda hadisin Jibrilu yake kunshe dasu, kuma martaba tafarko daga martabobin addini, itace martabar Musulunci, a musulunci kuwa rukuni na farko daga cikin rukunnansa shine shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma lallai Annabi Muhammadu (S.A.W) manzon Allahne.

Thursday, July 24, 2014

DIMUWA TA KAMA YAN AREWA

بسم الله الرحمن الرحيم Dukkan halin da Musulmin arewacin Najeriya ke ciki ko kuma Arewacin ba kowa bane ya janyo hakan illa masu iko da yankin. Wallahi Tallahi, dukkan matsalolin dake damun yan Arewa kama daga matsalar tsaro wacce itace tafi damunmu har zuciya kan quncin rayuwa da rashin aikinyi, duk jagororin mune suka jefa mu a cikinsu, domin tsananin kiyayyar da suke mana. Amma abin haushi da takaici, sai kaga talaka da talaka dan uwansa suna fada da zagin juna akan wasu azzaluman yan siyasa, misali anan Kano inda nake; sai kaga talaka yana zagin dan uwansa akan yana son Kwankwaso, ko kuma yana zagin dan uwansa harda fada akan yana son Shekarau. Gaba dayansu idan ka dauke su ka dora a ma'auni na ilimi da hankali wanda babu siyasa, to zaka fahimci cewa yan gida daya ne, jirgi daya ne ya kwaso su, kwaryar sama ce data kasa dan juma ne da dan jummai. Shugabanninmu na Arewa basa son mune, bawai iya mulki bane basuyi ba ko kuma Kudu sun fisu ne, a'a ko kadan sudai sun zabi zalunci ne halin dabbobi kawai. Idan akace gwamnatin tarayya tana bukatar kowanne bangare ta hannun mahukuntansa ya tura da mutane wadanda suka cancanta za'a basu aiki, to ina mai tabbatar muku da cewa dukkan wanda ya dace shi mahukuntan Kudu zasu tura matukar dai nasu ne, babu ruwansu da cewa daga wane gida yake ko kuma dan waye. To amma mu anan Arewa haka abin yake? Nasan dukkan mai hankali zaice a'a, dan hakane ma har muka samu wata kalma " sai kana da hanya" ko kuma ace " god-father" . To idan baka da wannan god-father din ko kuma hanyar, duk cancantarka da aikin bazaka samu ba, akan su tura ya yan talakawan gara subar offer din ta lalace a banza. To karku manta fa, takwarorinmu na Kudu sufa tuni sun aika nasu mutanen kuma watakila ma suna neman a kara musu damar. Ko a Taron Kasan nan, lokacin da akace kowanne bangare ya tura wakilai, meye ya faru? Sai gashi shugabanninmu sunki daukar abin da muhimmanci, sun tsaya jan kafa suna adawa da Taron saboda Goodluck ne ya kirkiro shi. Cikin masu adawa da taron har da manyan mutane wadanda har yanzu kimarsu na nan a idon jama'a, kamar Janar Buhari da Kwankwaso, suka rika cewa ai taron shan shayi ne, ai barnar kudi ne. To yanzu gashi nan yan Kudu sunfi mu yawa kuma sunfi mu kawo bukatu, kuma an gama taron. To ajema taron shan shayin ne, mu bamu iya shan shayin bane? Kowanne wakili abinda za'a bashi idan an gama taron (N 7,000,000), to ko dan muma yankinmu ya samu ai a tura da yawa ko? To mugunta da zalunci da dabbanci sun hana mahukuntanmu su tura mu, sai suka zabi yaransu da abokansu kawai. Ya Allah kayi mana maganin dabbobin shugabannin Arewa. Ya Ubangiji ka azurtamu da shugabanni masu adalci da tsoronka, masu kishin talakawansu, masu kare mutuncin jama'arsu da addininsu ameen.